Alhamis 4 Yuni 2026 - 17:13
Ayatullah al-Uzma Fayyadh, Daya Daga Cikin Manyan Maraji'an Najaf Ya Rigamu Gidan Gaskiya

Hauza/ Ayatullah al-Uzma Sheikh Muhammad Ishaƙ Fayyadh, daya daga cikin manyan maraji'an birnin Najaf mai alfarma, ya rasu a safiyar yau Alhamis bayan ya kwashe lokaci mai tsawo yana fama da rashin lafiya.

A cewar rahoton sashen fassara na Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, Ayatullah al-Uzma Sheikh Muhammad Ishaƙ Fayyadh ya riga mu gidan gaskiya ne yana da shekaru 96 a duniya a daya daga cikin asibitocin babban birnin kasar Iraki, wato Bagadaza.

Hazrat Ayatullah Fayyadh (wanda aka haifa a shekarar 1930 a kasar Afganistan), yana daya daga cikin manyan maraji'an taƙalid na mabiya mazhabar Shi'a Imamiyyah, kuma babban malami mai koyar da karatun koli na "Darsul-Kharij" a makarantar Hauzar Najaf mai alfarma, sannan ya kasance daya daga cikin almajiran fitaccen malami marigayi Ayatullah al-Uzma Sayyid Abul Qasim al-Khu'i.

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha